An Hana Jirage Masu Saukar Angulu Tashi daga Abuja

Mai ba shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro yace an hana jirage zirga zirga a Abuja sabili da dalilan tsaro har sai an kammala gyaran filin saukar jiragen saman birnin.

Wasu kamfanonin zirga zirgan jiragen sama ne suka shirya wa fasinjojinsu kananan jirage masu tashin angulu domin su dinga kaisu Kaduna daga Abuja inda zasu shiga manyan jirage zuwa kasashen waje saboda gyaran da a keyi a tashar ta Abuja.

To saidai mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro yace bisa dalilan tsaro ba'a yarda jiragen masu saukar angulu su dinga tashi ko sauka a birnin Abuja ba har sai lokacin da aka kammala gyaran filin jiragen saman birnin. A lokacin ne za'a bar kananan jiragen suna tashi da sauka a tashar.

A cewar wani tsohon hafsan hukumar leken asirin sojan Najeriya Aliko El Rashid Haroun matakin tsaro ne da ya dace. Yace yanzu jami'an tsaro sun tabbatar cewa kananan jiragen tsaro masu tashin angulu kadai ne suke da izinin tashi da sauka a birnin Abuja. Wadanda ba na jami'an tsaro ba sai sun nemi izini. Saboda matsalar tsaro wajibi ne a dauki irin wannan matakin, inji Haroun.

Kazalika ofishin mai ba shugaban kasa shawara akan harkokin tsaro ya ja hankalin wadanda suke da muradin kai komo ta sama daga Abuja da su kara hakuri har sai an gama gyaran filin Abuja.

Injiniya Muhammad Kyari Sandabe yana cikin masu yawan yin bulaguro ta sama yace idan aka ce abu zai kawowa kasar cikas akan harkokin tsaro dole ne a hakura dashi.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Hana Jirage Masu Saukar Angulu Tashi daga Tashar Abuja Zuwa Kaduna - 2' 13"