An hana bisne dan bindigar kasar Faransa mai tsattsauran ra'ayin addini a kasarsa ta ainihi, Aljeriya

Mohammed Merah kenan lokacin ya na raye.

Hukumomin kasar Algeria sun hana iyalan Ba-faranshen Dan

Hukumomin kasar Algeria sun hana iyalan Ba-faranshen Dan bindigar nan da ake zargi da laifin kashe mutane bakwai, da a binne gawarsa a hubbaren asalin iyalinsa dake Algeria.

Yau Alhamis naka ji wani babban jagoran Musulmi a Faransa,Imam Abdallah Zekri na cewa hukumomin Algeria sun ki amincewa da bukatar da iyalan Mohammed Merah suka gabatar ta neman iznin binne gawar danuwansu a makabartar iyalinsa dake Algeria, amma saboda dalili na tsaro.

Yace yanzu an shirya binne Merah a wata makabartar Musulmin dake birnin Toulouse kasar Faransa a yau Alhamis.

Tun a farkon wannan watan aka kashe Merah da ruwan harsasai, bayan ya ja daga da 'yan sanda na tsawon sama da sa'o'i 30 a gidan da ya ke haya a Toulouse.

Dan bindigar wanda hukumomi su ka ce ya yi ikirarin alaka da al-Qaeda ya amsa cewa ya kashe sojoji uku, da wasu yara 'yan makarantar Yahudawa su uku da kuma wani shugaban addinin Yahudawa.