Wani mai maganin gargajiya Usman Saidu mai shekaru 45 dake kauyen Kakumi a karamar hukumar Bakori dake jihar Katsina ya shiga hannu hukuma bisa zargin laifin hadin baki da kisa.
Mai maganin ya bawa wani matashi Aliyu Yahuza mai shekaru 27, a kayen Gobirawa dake karamar hukumar Safana maganin bindiga a ranar 22 ga watan Disambar 2017.
Sufeton ‘yan sanda Sani Ado ya shaidawa kotun Magistre dake Bakori cewa bayan Yahuza ya sha maganin sai aka kawo bindiga domin a gwada aikin sa a lokacin Usman yayi amfani da ita ya harbe shi a kirji abinda yayi sanadiyyar mutuwarshi a take.
A cewar sufeton an garzaya da Yahuza zuwa asibitin Dutsinma a inda likitoci suka shaida cewa ya rasu. Ya kara da cewa an dauki hoton gawar kamin daga bisani aka mika ta ga ‘yan uwanshi domin binnewa.
Sufeton ya ce laifin ya sabawa sashi na 97 da 222(7) na dokokin kasa da akafi sani da Penal Code ya kuma shaidawa kotu cewa ana ci gaba da binciken lamarin inda ya nemi a daga karan kuma kotu ta amince.
Hajiya Falila Dikko dake kotun ta bada umarnin a ci gaba da rike wanda ake zargin har 22 ga watan Febrairu lokacin da za’a ci gaba da saurarar karar.