Fada ya barke jiya Asabar tsakanin dakarun gwamnatoci biyu masu jayayya a Libiya a kokarin da kowanne daga cikin bangarorin biyu ke yi na mai da Tripoli, babban birnin kasar a karkashin ikonsa. An yi ta barin wutar atilari kan filin jirgin sama daya tilo da ke aiki a Tripoli, ta yadda wuta ta yi ta kama tankokin man jirage samufurin jet baya ga jiragen fasinja da aka lalatar, a cewar hukumomi a yammacin kasar ta Libiya da kuma Majalisar Dinkin Duniya.
Ma’aikatar Sufurin kasar mai hedikwata a birnin Tripoli ta ce daya daga cikin jiragen da aka lalata, dama zai tafi kasar Spain ne ya kawo wasu ‘yan kasar ta Libiya da su ka makale sanadiyyar kullen corona. Ma’aikatar ta dora laifin aukuwar hakan kan mayakan da ke gabashin kasar, wadanda su ka shafe sama da shekara guda su na kokarin kwace babban birnin kasar.
Kasar ta Libiya ta kasance cikin rudami tun a 2011, lokcin da wani yakin basasa ya yi sanadin tunbuke dadadden shugaba mai kama karya Moammar Gaddafi, wanda daga bisani aka kashe. Tuni kasa ta dare gida biyu karkashin gwamnatoci biyu kishiyoyin juna da ke gabashi da kuma yammacin kasar, kuma kowacce na da kungiyoyin mayaka da gwamnatocin kasashen waje da ke mara mat abaya.