An Gurfanar Da Manyan Sojojin Najeriya Gaban Kuliya Bisa Ga Laifin Gazawa

Sojojin da ake zargi da kin zuwa Arewa maso gabacin kasar domin yakar masu tsassauran ra'ayin addini sun hallara a gaba kotun Soja a Abuja, 2 ga Oktoba 2014.

A jiya Litinin ne dai aka gurfanar da hafsoshi da jami’an sojoji guda ashirin da uku a gaban kotun soji a birnin Lagos, dalilin zarginsu da ake da gazawa da tsoron ‘yan kungiyar Boko Haram.

Boko Haram dai sun kai hari ranar biyu ga watan Satumba na bara, wanda har suka sami nasarar korar sojojin Najeriya dake barikin soji a garin Bama a jihar Borno. Sojojin da suka hada da me mukamin birgediya janal daya, kanal kanal guda hudu, lutanal kanal guda bakwai, harma da wasu manyan sojoji su goma, ana tuhumar su ne da rashin tsayawa su buga da ‘yan kungiyar Boko Haram, hakan ne yasa ‘yan kungiyar suka kwace barikin sojojin ta garin Bama.

Wannan bashi ne lokaci na farko ba da aka gurfanar da sojojin Najeriya a gaban kotun soja ba, a bisa zargin kin tsayawa da fafatawa da ‘yan kungiyar Boko Haram, babban lauyan Najeriya dake kare Sojojin Femi Falana, yayi kira ga babban hafsan hafsosin Najeriya da yayiwa sojojin afuwa, inda yace a baya sojojin basu da wadatattun kayan aiki amma yanzu haka suna dasu kuma suna samin nasara akan yakin ‘yan kungiyar Boko Haram. Wannan shine karon farko da aka gurfanar da wani mai mukamin birgediya janal da kanal kanal a gaban kotun soja bisa laifin rashin iya aiki, gazawa da sakaci.

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Gurfanar Da Manyan Sojojin Najeriya Gaban Kuliya Bisa Ga Laifin Gazawa - 2'12"