An Guntulewa Wani Matashi Hannu

Wasu matasa sun guntulewa wani matashi hannu a garin Uyo babban birnin jihar Akwa Ibom, a lokacin da yake kokarin sace wani talebijin a wurin kallo.

Shi dai wannan matashi, an kama shine dab yana satar na talebijin din a inda matasa ke kallon wasani kwallon kafa, suka ko yi mashi cha a fusace.

Wani wanda akayi abin a idon sa ya ce wanda ake zargin ya je wajen kallon da yake Layin Ibiam, da misalin karfe biyar na asuba inda yayi kokarin sace talebijin,din amma wani ya ganshi ya kuma yi kara.

Jin wannan kara sai matasa suka ce da wa Allah ya hadasu suka bi shi suka ko cim mashi aka nakada mashi duka, bayyana ‘yan Sanda ne ya ceceshi da sun kashi, amma karfin ‘yan Sanda su bayyana an riga an guntule mashi hannu.