An Gudanar Da Bukin Sabon Sarkin Dogarawan Abzin, Nijar

Bukin Sarkin Dogarawan Abzin, Nijar

A Janhuriyar Nijar mai cike da al'adu iri-irir, an nada Sarkin Dogarawan Abzin a wani kasaitaccen da ya burge masu wannan al'adar da kuma 'yan kallo.

A karkashin jagorancin ministan cikinn gida ne na Nijer cewa da Bazum Mohamed a ka gudanar da wani wagegen buki a garin Dogarawa tareda halartar ministocin ruwa da tsabta da na hanyoyi da yan majalisun dokoki na kasa da gwamnan jahar Tahoua da shugabanin gundumomi da dama da mafi yawancin manyan sarakunan gargajiya na Nijer, domin halartar askin sarautar basaraken Abzin ta Dogarawa, daya daga cikin mafi muhimancin masarautun masu babban tarihi a kasar.


Na tambayi Abdu Kadri basaraken da aka yiwa askin sarauta, domin jin, ko shirye yake ya karbi gaskiya komi dwacin ta daga fadawan sa? ganin cewa, a Africa, a mafi yawancin lokaci, koda shugaba na kan laifi ko kuskure, kowa na tsoron fada masa gaskiya....


Dimbin mutane ne maza da mata, suka halarci taron, abinda ya sa na tuntubi malam Ahmed Suleymane Dan Majalisar Dokoki na kasa mai wakiltar mazabar Birni N'Konni gameda yanda suka ga taron.....


Sarkin dake kasancewa na 6 a masarautar Abzin ta Dogarawa dake tsakiyar kasar, ya samu kiaukiawan fata daga talakawan sa da suka nuna murnar su na ganin wannan ranar.

Your browser doesn’t support HTML5

Bukin Masarautar Dogarawa a Jihar Tahoua