An Gudanar Da Taron Zaman Lafiya Da Tsaro a Matsugunan Musulmin Ghana Domin Cimma Manufar Raya Cigaba Na MDD Mai Dorewa

Taron Zaman lafiya

A yunkurinta na neman bada nata gudunmuwa domin cimma manufofi raya cigaba na majalisan dinkin duniya mai dorewa kafin shekarar 2030, gwamnatin Ghana ta dau nauyin shirya shirya taron jaddada muhimmancin zaman lafiya.

Gwamnatin Ghana ta shirya taron samar da tsaro tare da zaman lafiya amatsugunin musulmin Ghana.

Wannan taro da hukumar raya cigaban zangwanin fadin kasar ta shirya a birnin Kumasi ya samu halartar masu ruwa da tsaki bisa harkar cigaban Musulmin Ghana kama daga yan siyasa da limamai da sarakuna da matasa tare da masu jan akalar tafiyar, iyaye mata.

Taron Zaman lafiya

Hon Ben Abdallah Banda babban jimi'in hukumar raya tsakiyar birane da zangwannin fadin kasar da ya wakilci Mataimakin Shugaban kasa ya bayyana cewa wannan na daga cikin gudunmuwar da gwamanatin Ghana zata bayar domin ganin an cimma wannan manufar.

Taro

Sai dai kuwa wakilin majalisan dattawa Hon Muntaka Mubarak ya bayyana cewa muddun ana bukatar zaman lafiya a Ghana ya kamata a yi ma alumman zango adalci musamman gurin kiyaye hakkokinsu tare da bai wa Musulmi damarmaki ba tare da nuna banbancin addini ba.

Shugaban Tijaniyya a Ghana, Sheikh Abdul Wadud Ciessay da ya kasance magakujerar taron ya jaddada tsokacin wakilin majalisan a inda yake cewa ba za a samu zaman lafiya da tsaro ba fashe an yi adalci da gaskiya.

To sai dai mataimakin shugaban izala a Ghana na bukatar da amaida hankali gurin samar ma matasa sana'o'in yi sabida galibin matasa, musamman masu ilimi, ba su da sana'o'i, inji shi.

Real Admiral Muniru TAHIRU tsohon shugaban kwalejn horas da dakarun soja a Ghana kana magakujerar kwamitin raya cigaban zango a Ghana ya bayyana cewa anfi anfani da da matasan zango gurin aikata muggan laifuka, abin da ya ce akwai damuwa sosai

Mai sharhi bisa harkar tsaron cikin da wajen Ghana Mallam Irbad Ibrahim na ganin kamata yayi da gwamnati ta ringa tallafa wa sarakunan zango kasancewa sune masu gwagwarmaya domin samun zaman lafiyan zango aGhana .

Magajiyan Zangon Kumasi Hajia memuna Nunu ta tofa nata albarkacin baki ainda take cewa iyaye mata da kananan yara ke wahala in babu zaman lafiya adon ta bukaci da ayi kokarin tabbatarda zaman lafiya da tsaro mai dorewa.

Mai rikon kwaryar masarautar zango a Kumasi, Alhaji Ibrahim Abdul Rahaman na bukatar da sarakuna su hada kai su kauce wa rarraba domin tunkarar wannan matsala

Yayin jawabinsa shugaban hukumar raya cigaban zango a kasar, Hon Arafat Sulaiman ya ce gwamnatinsa ta jamiyyan NPP ta inganta shirye shirye da dama na daga ciki gina makarantu, horar da matasa sana'o'in hannu, daukar dawainiyar karatun daliban zango, gina filayen murza leda irin na zamani. Ya ce wannan duk na daga cikin matakan tabbatar da zaman lafiya da tsaro a zangwannin kasar, amma kuwa za su cigaba da kara ayyukan domin ganin an shawo kan wannan matsala.

Matsugunan na daga cikin guraren da subka yi kauren suna gurin aiwatar da miyagun ayyuka irin su fadace fadace da sayar da miyagun kwayoyi masu tarwatsa hankullan bayin Allah da de sauransu. Abin da hukumomi ke kokarin kawo karashensu.

Saurari cikakken rahoton cikin sauti:

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanarda Taron Zaman Lafiya Da Tsaro a Matsugunan Musulmin Ghana Domin Cimma Manufar Raya Cigaban MDD Mai Dorewa