Masu zabe a kasar Mali dake yammacin Afrika sun fita jiya Lahadi don kada kuri’un zaben ‘yan majalisun kasar da aka dade ana jinkirtawa, wanda ya gudana a cikin yanayin fargaban tada kayar bayan ‘yan ta'adda da kuma annobar cutar coronavirus.
An bude rumfunan zaben ne 'yan sa’o’i bayan da jami'an kiwon lafiyar kasar suka ba da sanarwar mutuwar mutum na farko a kasar sakamakon cutar coronavirus. Yanzu jimlar mutum 20 ne suka kamu da cutar a Mali.
Tun da farko an tsara gudanar da zaben na jiya ne a shekarar 2018, amma aka dage gudanar da shi a lokuta da dama, a dalilin karuwar rashin tsaro a Arewaci da tsakiyar kasar ta Mali inda kungiyoyin ‘yan ta'adda masu alaka da kungiyar al-Qaida da kungiyar I.S suka karbe ikonsu a ‘yan shekarun nan.
Ko a makon da ya gabata an kai wani harin kwanton bauna kan jagoran ‘yan adawar kasar Soumaila Cisse da tawagarsa, a yayin wani gangamin yakin neman zabe a yankin Arewacin kasar. An kashe wani dogarin Cisse, yayin da aka sace shi kansa Cisse da wasu mutane su 6, har yanzu ba amo ba labarinsu.