Yanzu haka dai an gudanar da zaben sarkin Dogon Dutse dake cikin jamhuriyar Niger, wanda aka jima ana jayayya akan sa.
An dai gudanar da zaben ne cikin yanayi tsaro mai tsaurin gaske ganin yadda ake da rarrabuwar kawuna game da wannan al’amari.
Wakilin Sashen Hausa Sule Mummuni Barma ya tuntubi Aliyu Bawa wani Dan Jarida da ya gane wa idanun sa yadda wannan lamari ta kaya ya shaidawa Sulen cewa.
Zaben dai an gudanar dashi cikin kwanciyar hankali da lumana, domin daga cikin wadanda ya kamata su jefa kuri’a su 121, amma 76 ne suka halarci zaben, kenan 45 ba suyi zaben ba.
Kuma da farko ‘ya takara 14 ne suka fito domin neman wannan sarautar, amma kafin a fara zaben ‘yan takasra 5 suka janye, kenan ‘yan takara 9 ne suka fafata.
Har wayau cikin 9 ma daya daga cikin su bai zo wurin zaben ba. Don haka a cikin wadanda suka rage Abubakar Marafa ne shine yayi nasara.
Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani.
Your browser doesn’t support HTML5