An Gudanar Da Zaben Kananan Hukumomi A Jihar Plato

Wadansu mata suna jira su kada kuri'a a runfar zabe

An gudanar da zaben shugabannai da kansiloli a kananan hukumomi goma sha uku na jahar Pilato, cikin kwanciyar hankali da lumana.

Tun farko, hukumar zabe mai zaman kanta a jahar Pilato ta dakatadda zaben a Kananan hukumomin Jos ta Arewa, Jos ta kudu, Barkin Ladi da Riyom saboda matsalolin tsaro.

Zaben shine karo na biyar tun lokacin da aka shigo mulkin damokradiyya a shekara ta dubu da dari tara da tasa’in da tara.

Jami’iyu hudu ne suka shiga zaben da suka hada da ADP, GPN, APC da PDP.

Duk da shike ba a sami wata matsalar tsaro da tayi tasiri ba, an sami matsalolin rashin kai kayan zabe a rumfunan zaben cikin lokaci wanda ya sanya masu kada kuri’a basu fara zaben kan lokaci ba a wurare da dama, yayinda wadansu kuma suka bayyana cewa basu ga sunayensu ba a rajistar zabe.

Duk kokarin da Wakiliyar Sashen Hausa Zainab Babaji tayi na neman bayanin daga shugaban hukumar zabe mai zaman kanta a jahar Pilato, Mr Fabian Ntung yayin dauko wannan rahoton ya cimma tura.

Saurari cikakken rahoton.

Your browser doesn’t support HTML5

Zaben kananan hukumomi a Plato-3:00"