Filato: INEC Ta Gudanar Da Zabe a Wasu Rumfuna Biyu Yau Lahadi

Wasu 'Yan Bautawa Kasa Na Shirye-shiryen Fara Aikin Zabe

Hukumar zabe mai zaman kanta a Jihar Plateau, ta gudanar da zabe a runfuna biyu dake kananan hukumomin Jos ta kudu da Riyom anan Jihar Plateau.

Hukumar zabe mai zaman kanta a Jihar Plateau, ta gudanar da zabe a runfuna biyu dake kananan hukumomin Jos ta kudu da Riyom a Jihar Plateau.

Gudanar da zaben a yau lahadi ya biyo bayan mushkila ne da aka samu wajen hada sunayen masu kada kuri’a a runfar zaben “Zawan A” da wadanda ke da “Zawan B”.

Inda a Riyom kuwa da Attaakar da Uchan ba’a kai kayayyakin zabe da wuri ba, kuma aka samu sabani tsakanin masu ruwa da tsaki a yankin, wanda ya janyo sauya zaben zuwa yau lahadi.

Jami’in wayar da kan jama’a na hukumar zaben jahar Plateau yace yanzu haka sun shayo kan matsalar, kuma ana gudanar da zaben, kuma yace a mazabun Attakar da Uchan karamar hukumar Riyom, matsala aka samu da masu fada aji a yankin da ya sanya suka hana jami’an su saukar da kayyakin zabe a yankin, dalilin da yasa kenan aka dage zaben zuwa yau lahadi, Jami’in yace yanzu haka ana gunadar da zaben babu wata matsala.

Wakiliyar muryar Amurka Zainab Bababji ta zanta da wasu masu kada kuri’a a runfar “Zawan B” dake karamar hukumar Jos. inda suka ce kuskure ne aka samu daga hukumar zabe, amma yanzu ta gyara kuma sun kada kuri’unsu.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gudanar Da Zabe Yau Lahadi A Jos Ta Kudu Da Riyom 03'29"