An Gudanar Da Zabe a Mali Dukda Fargabar Coronavirus

An gudanar da zabukan majalisun Kasar Mali a jiya Lahadi kamar yadda aka tsara, duk da barazanar tashe-tashen hankula daga masu ikirarin jihadi da kuma tsoron yaduwar cutar nan mai kisa ta coronavirus.

Dama an yi hashashen rashin fitowar masu kada kuri’a a zaben na jiya Lahadi.

An gudanar da zagayen farko na zabukan ne a ranar 29 ga watan Maris, bayan da aka yi ta samun tsaiko wanda ya hada da barazana daga 'yan rajin jihadi da ya kai ga sace shugaban ‘yan adawa Soumaila Cisse.

Hukumomi sun ce Kaso 12 cikin dari na masu kada kuri’a ne suka fito a birnin na Bamako, inda mafiya yawan mutane suka zauna a gida domin bin umurnin hana taron jama’a da yawa da kuma bada tazara.