A safiyar yai Asabar aka fara gudanar da zabe a Myanmar, zaben na farko da ake ganin za’a gwada farin jinin jam’iyyar Aung San Suu Kyi mai suna National League for Democracy bayan shekara guda akan mulki.
WASHINGTON, DC —
Daruruwan masu zabe sunyi layi a wuraren kada kuri’a a yau Asabar a wajen babban birnin na Myanmar mai suna Yangon duk da cewa wurin babu hayaniya da kewa irin ta zaben da akayi na shekarar 2015 mai dinbin tarihi.
Masu zabe na kada kuri’un mazaunin Yan majalisa 19 na kasa da kuma na yanki.
Masu fashin baki sun ce akwai damuwa ta rashin aiwatar da sauye sauye, amma ana tsammanin masu zabe zasu cigaba da goyon bayan Aung San Suu Kyi da Jam’iyyarta.
Jam’iyyar NLD na da rinjayen kujeru a majalisar Myanmar wacce aka fi sani da Burma haka kuma ba’a tunanin zaben na yau Asabar zai sauya yanayin mulkin kasar.