Shuwagabanin kasashe 4 ne suka karbi goron gayyatar shugaban kwamitin yaki da illolin canjin yanayi a yankin Sahel Issouhou Mouhammadou na Nijer, a wannan taro dake samun halartar wasu shuwagabanin gwamnatocin kasashe da nufin nazari akan shawarwarin kwararru da ministocin kare muhalli wadanda suka shafe kwanaki biyu suna tattaunawa a birnin Yamai dake Nijer domin neman mafitar halin da canjin yanayi ya jefa wannan yanki.
A cewar Mahamadou Issouhou mai masaukin baki, illolin canjin yanayi ne musabbabin akasarin matsalolin da nahiyar Afirka ke fuskanta a yau, missali shi ne yawaitar kafuwar kungiyoyin ta’addanci da tsanantar zuwa ci ranin matasa a sakamakon rashin madogara. Ya kara da cewa, a saboda haka ya zama wajibi kasashen duniya su tashi tsaye a bisa la’akari da gargadin da masana ke bayarwa.
Shugaban kwamitin yaki da illolin canjin yanayi a yankin manyan tafkuna Denis Sassou Nguesso na kasar Congo Brazzaville ya bayyana cewa illolin canjin yanayi wani abu ne da ake iya magancewa muddin aka dage. Akan haka ya shawarci takwarorinsa na Sahel akan su yi koyi da ayyukan dashen itacen da kasar Congo ta kaddamar daga gabar kogin Atlantika zuwa kogin Maliya ratsawa ta Senegal da Djibouti.
Ministan kare muhalli jamhuriyar Nijer Almoustapha Garba ya sanar cewa taron ministocin da ya gudana a jajibirin wanda shuwagabanin kasashe ke gudanarwa a yanzu haka ya jaddada bukatar gudunmuwar manyan kasashe wajen hada kan kudaden da za a tunkari illolin canjin yanayi a karkashin tsarin PIC RS na tsawon shekaru 12.
Kungiyoyi masu zaman kansu dake kallon wannan taron da muhimmanci sun ja hankulan shuwagabanin akan bukatar a yi adalci wajen tafiyar da tallafin da ake hasashen samowa daga masu hannu da shuni.
A gobe tallata ne za a ji matsayin masu hannu da shuni a dangane da alkawalin da suka dauka a taron Paris na shekarar 2015.
Your browser doesn’t support HTML5