An Gudanar Da Taron Neman Zaman Lafiya A Niger

Ministan Cikin Gidan Nijar da sauran manyan jami'an gwamnati a wurin taron kolin tsaron da aka gudanar.

Gwamnatin Nijar ta bayyana damuwa a kan yadda matsalar 'yan bindiga ta ki karewa a cikin kasar da kuma yaduwar kananan makamai a tsakanin jama'a ganin yadda hakan ya ke da illa musamman ga mata da kananan yara.

Bijiro da wannan batu dai a wani taron zaman lafiya na kasa da aka gudanar a Agadas ya dada haskaka yadda kasashen yankin sahel ke fama da wannan matsalar ta rashin tsaro da kuma bazuwar makamai.

Duk da irin kokarin da ake yi wajen samar da tsaro, har yanzu ana cigaba da kara kaimi a wasu yankuna na ciki da wajen Nijar, makasudin kenan da ya sa aka gudanar da wani taro na majalisar koli kan sha’anin tsaro karkashin jagorancin ministan tsaro da ministan cikin gida na kasar Nijar don samun hanyoyin magance matsalar tsaro a Nijar dama yankin sahel baki daya.

Tun farkon hawan karagar mulkin kasar Nijar, shugaba Bazoum Mohammed ke fatan ganin yayi anfani da hanyoyin tattaunawa a fannoni da dama wajen shawo kan matsalolin tsaron da suka addabi yankin.

Jami'an Tsaro A Wurin Taron Kolin Neman Zaman Lafiya A Nijar

Alkasum Indatu, Ministan tsaron kasar Nijar ya bayyana cewa an shirya taron ne bisa umarnin shugaban kasar na Nijar wanda ya bukaci su tattauna al'amuran da suka shafi tsaro da zummar samun hanyoyin magance su.

Ganin yadda 'yan bindiga suke salwantar da rayukan jama’a da dukiyoyinsu yana tayar da hankali kuma saboda hakane shugaban kasa ya tura irin wannan tawagar domin yin duk abinda ya dace don maido da zaman lafiya a yankin.

Mininistan cikin gidan Nijar Hamadu Sule ya tabbatar da daukar matakkan da suka dace domin ganin bayan wannan matsalar ta tsaro.

Jami'an Tsaro A Wurin Taron Kolin Zaman Lafiya A Njiar

Yayi bayanin cewa salon harkar tsaro a wannan yankin lamari ne dake tada hankali matuka a Agadas wanda yake da iyaka da kasashen Mali, Libiya, Algeria da sauransu lamarin da a tsakar rana ana tare mutane wani lokaci harda kisa, kuma bisa wannan dalili ne ake kokarin samun maslaha game da abinda ke faruwa musamman bazuwar makamai a hannun jama’a ba bisa ka’ida ba, ya kuma kara da cewa, ya san cewa jami’an tsaro na iya bakin kokarinsu amma yana da mahimmanci a taru domin kawo karshen wannan matsalar.

Kungiyoyin fararen hula a Nijar sun bukaci gwamnati su tashi haikan wajen shawo kan matsalar yan bindiga da ke hana su sakat. Saurari cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

RAHOTON TARON KOLIN TSARO.mp3