Kungiyar ta hada wani taro a yankin Afaka da ke garin Kaduna, inda aka tattara mabanbantan addinai da kabilu don jawo hankalin al’umma su fahimci banbance-banbancen da ke tsakaninsu don su zauna lafiya da juna.
‘Daya daga cikin shugabannin kuniygar GPF, Rev Joseph Hayaf, ya ce idan an daina nuna banbancin addini da na kabila a tsakanin mutane za a samu cikakkiyar zaman lafiya da samun ci gaba.
Shima Sheikh Halliru Maraya, dake zama shugaba a kungiyar GPF, ya ce sun lakanci bayan addini al’ada na matukar taimakawa wajen samun fahimtar juna, inda yace babu yadda za a sauna lafiya ba tare da an fahimci asali ba.
Da yawa daga cikin halarta taron sun nuna jin dadinsu da godiyarsu ga muhimmancin wannan taro, wanda ya hada Musulmai da Kristoci da kuma kabilu kala daban-daban, domin samar da hadin kai da tabbatar da zaman lafiya.
Domin karin bayani saurari rahotan Isah Lawal Ikara.
Your browser doesn’t support HTML5