Za a gudanar da zaben ne domin cike gurbin tsohon kakakin majalisar dokokin jihar Taraba, Haruna Tsokwa
WASHINGTON, DC —
An girka jami'an tsaro da yawa a yankin karamar hukumar Takum ta Jihar Taraba, inda a yau asabar za a gudanar da zaben cike gurbin tsohon kakakin majalisar dokokin Jihar Taraba, marigayi Haruna Tsokwa.
Kakakin rundunar 'yan sandan Jihar Taraba, DSP Joseph Koje, yace an tura isassun jami'an tsaro wadanda zasu yi gadin dukkan rumfunan zabe da mazabu domin tabbatar da cewa komai ya tafi lafiya.
Shi ma Kwamishinan hukumar zabe a jihar Taraba, yace sun kammala dukkan shirye-shiryensu, kuma har sun kai kayan aiki da ma'aikata zuwa karamar hukumar ta Takum, inda tun a jiya jumma'a suka fara rarraba kayan zaben ga jami'an da zasu gudanar da shi.
Manyan jam'iyyu uku suke takarar wannan kujera, cikinsu har da APC ta adawa da kuma jam'iyyar PDP wadda take rike da kujerar kafin rasuwar tsohon kakakin majalisar dokokin ta jihar Taraba, Haruna Tsokwa. A yanzu ma, kanin marigayin ne jam'iyyar ta PDP ta tsayar a zaman dan takararta a wannan zaben.
Ga rahoton Ibrahim Abdul'aziz daga Jalingo

Your browser doesn’t support HTML5