An Gina sabon Asibitin Mata a Jihar Neja

Gwamnatin jihar Neja ta gina wani sashen kula da mata masu juna biyu da yara, a wani mataki na rage cunkoson marasa lafiya na asibitin gwamnatin jihar Neja dake Minna.

Gwamnatin dai tace ta dauki wannan matakin ne bisa la’akarin yawan jama’ar dake kara kwararowa zuwa jihar.

Kwamishinan yada labaran jihar Alhaji Danladi Ndayebo ya fadi cewa yawan tashe-tashen hankulan dake faruwa a wasu jihohin dake kusa da su, ya kawo cinkoso. Shiya sa suka yanke shawarar yin sabon asibiti musamman na mata masu ciki kuma kwanan nan za a kaddamar da shi.

Kwamishiniyar kiwon lafiyar jihar Hajiya Hadiza Abdullahi tace sabon asibitin da suka so kamalawa tun a watan Disambar bara, zai maida karfine akan mata masu juna biyu.

Duk da yake samar da wannan asibiti ya zo ne a daidai lokacin hada-hadar siyasa, masana sun yi imanin cewa zai taimaka wa mata dake samun matsaloli wajen haihuwar wanda har ma akan rasa rai.

Your browser doesn’t support HTML5

An gina sabon asibitin mata a jihar Neja - 2'32"