An gano wasu nau'in kwayar halitta dake hana kamuwa da zazzabin cizon sauro

Wata karamar yarinya mai fama da zazzabin cizon sauro

Masu ilimin kimiyya a kasar Jamus da Afirka sun bayyana cewa, sun gano wadansu nau’in kwayar halittar mutum da suke hana kwayar cutar zazzabin cizon sauro kwantar da wadansu mutane.

Kwararrun sun gano haka ne bayan gwada jini da kwayar halittar sama da mutane dubu a kasar Ghana wadanda zazzabin cizon sauro ya kwantar da wadansu mutane dake cikin koshin lafiya.

An kwatanta sakamakon binciken da aka gudanar karkashin Christian Timmann, wani jami’I dake aiki a makarantar binciken magunguna a kasashe masu zafi, Benhard Noctch Institute dake Hamburg kasar Jamus, da wanda aka gudanar a kasar Gambiya tsakanin kananan yara.

Bincike da aka gudanar a lokutan baya, na nuni da cewa, mutanen da suke da nu’in jinni rukunin “o” suna da kariya daga nau’in kwatar cutar zazzabin cizon sauro da yafi tsanani da ake kira “falciparum malaria”. Yayinda aka kuma tarar mutanen dake da cukar sikila ba safai suke kamuwa da zazzabin cizon sauro ba

Rahoton Hukumar Lafiya ta Duniya na shekara ta dubu biyu da goma na nuni da cewa, kimanin mutane miliyan dari biyu da goma sha shida ne suka kamu da zazzabin cizon sauro, daga ciki mutane dubu dari shida da hamsin da biyar suka rasu, akasarinsu kananan yara a nahiyar Afrika.