An Gano Wasu 'Yan Damfara 'Yan Najeriya Guda Biyu A Amurka

Kusan shekaru hudu kenan, ‘yan damfara da yawa daga Najeriya da kuma wasu kasashen suka sace miliyoyin kudade daga hannun jama’a da kamfanoni a Amurka, suna sanya kudaden a asusun bankunan wasu ‘yan Najeriya su 2 dake zama a birnin Los Angeles dake jihar California a Amurka.

A yayinda damfara ta yanar gizo ke karuwa sosai, wasu ‘yan Najeriya Velentine Iro da Chukwudi Christogunus Igbokwe sun yi kaurin suna a wannan sana’ar, kuma sun yi amfani da lakanin sunaye dabam dabam, ciki har da "Iro Enterprise da Chris Kudon.”

Tsakanin shekarar 2014 da 2018, Iro da Igbokwe, da wasu ‘yan damfarar a kasashen waje kusan su tamanin da suka yi aiki tare, suka taimaka wajen kitsa damfara lokuta dabam dabam da kudin suka kai akalla dala miliyan shida, bayan haka suka kuma yi yinkurin satar karin dala miliyan arba'in daga wasu mutanen a kasashe fiye da goma, a cewar wasu takardun binciken mashara’antan gwamnatin tarayyar Amurka.

A shekarar 2014, wani mai harkar saida tufafi a birnin San Diego ya tura kudi kusan dala dubu arba'in da shida ta yanar gizo zuwa wani asusun banki dake mallakar daya daga cikin ‘yan damfarar, bisa zaton wani dan kasuwar kasar China ya turawa kudin akan odar wasu rigunan sawa na maza.