An Gano Wasu Kaburbura a Malaysia

Wasu bakin haure da ke kokarin ketara teku domin neman mafaka a kasashe masu galihu

Yayin da ake fama da matsalar kwarar bakin haure masu neman mafaka a kasashe masu galihu, hukumomin Malaysia sun ce 'yan sanda sun gano wasu manyan kaburbura cike da kasuwuwan mutane.

Hukumomi a kasar Malaysia sun ce ‘yan sanda sun gano wasu manyan kaburbura dauke da gawarwakin da ake tunanin na bakin haure ne daga Myanmar da Bangladesh.

Ministan cikin gida, Zahidi Hamidi, ya gayawa manema labarai cewa, an gano kaburbura ne a kan iyakar kasar da Thailand, a kusa da wasu kauyuka da ake safarar mutane.

Kafafan yada labaran kasar sun ce kaburburan sun kai 30, wadanda ke dauke da daruruwan kasusuwan mutane a kusa da wasu sansanonin da masu safarar mutane ke amfani da su.

A baya hukumomin kasar ta Malaysia, sun musanta ikrarin da ake na cewa akwai ire-iren wadannan kaburbura a kasar.

A gobe Litinin ake sa ran shugaban rundunar ‘yan sandan kasar zai yi jawabi ga manema labarai kan wannan batu.