An Gano Wani Wakilin VOA Hausa Na Boge a Jihar Kebbi

Muhammad Tukur Usman

Sashen Hausa na muryar Amurka ya gano wani mutum mai suna Muhammad Tukur Usman Wanda ke zaune a garin Yawuri na jihar Kebbi Wanda ke ikirarin yana aikawa sashen Hausa na Muryar Amurka rahotanni, amma yaudara ce kawai.

Asirin Muhammad Tukur wanda ake ake kira "Mallam Ango" ya tonu ne lokacin da yake shirin yaudarar wata kungiya mai zaman kanta wadda ke aikin kyautata rayuwar mata da kananan yara a jihar Kebbi, lokacin da su ka je gudanar da taruka a garin Yawuri.

Daya daga cikin shugabannin kungiyar da Sashen Hausa ya yi hira da ita, wadda ta nemi a saya sunanta ta ce, lokacin da suka isa garin suka nemi a hada su da manema labarai domin su dauki rahotannin ayyukan da za su gudanar domin a yayata, shine aka shaida masu cewa, akwai wani wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka aka kuma kira shi ya je wurin.

Shugabannin wannan kungiya sun fara tunanin akwai matsala ne bayanda wakilin bogen ya bayyana masu hanyar da zasu iya sauraron rahoton nasu da kuma dalilansa na neman kudi daga gare su. Wannan ya sa suka nemi ganin shaidar shi wakilin Muryar Amurka ne, suka kuma tuntubi wakilin Sashen Hausa da ke garin Sokoto domin neman tantance sahihancin bayanin wakilin boge.

A cikin hirarsu da wakilin Sashen Hausa na muryar Amurka na jihar Kebbi Muhammad Nasir bayan samun bayanin wannan mutumen da ya zanta dashi ta wayar salula, wakilin bogen ya nemi a biya shi naira dubu hamsin kafin ya aika rahoton, bayan sun yi ciniki ya amince a biya shi naira dubu arba’in ya kuma turawa wakilin Sashen Hausa lambar bankin da za a tura mashi kudin.

Saurari cikakken rahoton Muhammad Nasir cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Gano Wani Wakilin VOA Hausa Na Boge a Jihar Kebbi:3:15"