Shugaban rundunar Abdullahi Ibrahim, ya ce an samu littafin ne a dakin saukar baki na Dikwa wanda mallakar gwamnati ne.
Sai dai Ibrahim ya ki yin karin bayani kan yadda suka gano littafin, amma a cewarsa, wannan littafi da shi mayakan na Boko Haram su ke yin amfani wajen sauya tunanin mabiyansu.
“A ciki ake nunawa mutum idan ka yi amfani da wannan (littafi) harsashi ba zai huda ka ba, kuma idan aka kawo maka hari za ka bace, sannan idan ka je saka bam, idan ka saka sai ka bace.” Inji Ibrahim.
Ya kuma kara da cewa sun mika littafin ga malamai wadanda suka yi bincike akai, suka kuma gano cewa irin wannan siddabarun al’umar Banduma da ke kasar Chadi ne ke amfani da shi.
Domin jin cikakkiyar hirar, saurari ganawar wakilin Muryar Amurka, Haruna Dauda Biu da Abdullahi Ibrahim:
Your browser doesn’t support HTML5