Jami'an kiwon lafiya na matakin farko a Nigeria suna koyas da mata yadda ya dace su kula da cibiyar jariransu bayan an yanke mahaifa.
Bayan taron makon shayar da jarirai nonon uwa a Abuja hukumar kiwon lafiya matakin farko ta wayar da kawunan mata su daina anfani da sinadarin spirit wanda yake sanya jariri barci. Wannan ya biyo bayan samun wani sabon magani ne da kan yi tasiri wajen tabbatar da lafiyar jariri da kuma tsafta.
Dr. Rukayya Wamako darakta mai kula da sashen rigakafi na hukumar kiwon lafiya a matakin farko ta ce cibiyar jariri sabon haihuwa idan a shafa mata spirit tamkar an shafa masa sinadarin giya ne domin barci zai ta yi saboda yana tsotsa ta cibiyar. Baicin hakan sinadarin spirit idan an yi kusa da wuta ya kan maka wutar.
An yanke shawarar daina anfani da spirit domin shi wannan sabon maganinda aka kira "Chlorhexidine Gel" ya na da saukin aiki fiye da spirit.
Dr Rukayya Wamako ta ce hukumar kiwon lafiya ta duniya cewa ta yi idan an wanke cibiyar jariri a barta haka amma a gargariyance sai a dauki kashin kaji ko na shanu ko sabulun wanke baki da dai sauransu. Ta ce duk sai ya kawo wata cuta ma yaro.
Dr Wamako ta ce wannan sabon maganin an tabbatar bashi da wata cuta ko illa kana yana kare jariri daga wasu cututuka.
A saurari rahoton Hauwa Umar Udubo
Your browser doesn’t support HTML5