An Gano Sabban Alamun Makabartun Dinbin Jama'a a Sudan

  • Ibrahim Garba

'Yan gudun hijiran Sudan a Kadugli.

Wata cibiyar dauko hotuna da tauraron dan adam da ke nan Amurka ta ce ta hango sabbin

Wata cibiyar dauko hotuna da tauraron dan adam da ke nan Amurka ta ce ta hango sabbin alamun makabartun dinbin jama’a a yankin Kordofan ta Kudu mai arzikin man fetur.

A yau Laraba, cibiyar “Satellite Sentinel Project” ta gabatar da bayanan shaidun gani da ido da kuma hotunan abin da ta bayyana da cewa na’urorin tono ne da kuma jakunkunan saka gawa da kungiyar agaji ta Red Crescent ta Sudan ta yi amfani da su wajen tono da kuma biso a wadannan makabartun.

Cibiyar ta ce a yanzu ta gano jimlar makabartu 8 a yankin, ciki har da guda biyun da aka bayyana su a yau dinnan.

Gwamnatin Sudan dai ta karyata bayanin wannan cibiyar. Gwamnatin ta aza alhakin tashin hankalin wannan yankin kan kungiyoyin ‘yan tawaye da kuma sojojin sabuwar kasar Sudan ta Kudu.

A jiya Talata, Shugaban Sudan Omar al-Bashir ya yi kiran da a tsagaita wuta na tsawon sati biyu a Kordofan ta Kudu. Da ya ke magana a Kadugli, babban birnin wannan jiha da ke kan iyaka, Shugaba Bashir ya ce za a tantance abubuwan da su ka faru ne bayan yarjajjeniyar tsagaita wutar.