An gano ma’aikatan boge fiye da dubu ukku da dari hudu a ma’aikatar kananan hukumomi na jihar Abia, wadanda ke karbar albashi daga lalitar Gwamnatin jihar.
Jihar nada kanana hukumomi goma sha bakwai, da ma’aikata fiye da dubu goma sha bakwai da dari takwas, da albashin miliyan dubuda dari takwas.
Ma’aikatan bogen sun hada da fiye da dubu ukku da dari takwas, da suka gasa nuna takardan shedar daukansu aiki da wasu dari ukku da sittin da ukku, wadanda hukumar jarabawa ta yammacin Afirka, tace sakamakon kammala jarabawar tasu ta buge ce da kuma wadanda yakamata sunyi retaya sun dari biyu da arba’in da shida, amma suka canja shekarunsu da kuma wasu dari daya da tamanin wadanda aka ragewa girma.
Wannan na kunshe ne a cikin sakamakon bincike da kwamitin mutane goma sha biyar da Gwamnatin jihar ta kafa karkashin jagorancin tsohon kakakin majalisar jihar Mr. Alwell Asiforo.
Kwamiktin tace ta gano abu mai ban takaici inda aka sami mutun daya ya karbar albashi na mataki goma sha hudu a asibitin Amachara, dake Umuahia, har ila yau kuma yana karbar wani albashin a karamar hukumar Umuahia ta kudu a matakin albashi na goma sha ukku, a duk watan duniya.