An Gano Karin Gawawwaki 2 Daga Hatsarin Jirgin Shelkwafta Na Fatakwal - NSIB

Hukumar binciken afkuwar hadura ta Najeriya (NSIB) ta bayyana cewar an gano karin gawawwaki 2 daga jirgin saman shelkwafta kirar Sikorsky S-79 da ya yi hatsari a birnin Fatakwal, fadar gwamnatin jihar Ribas.

Babban daraktan NSIB, Alex Badeh, ne ya bayyana hakan a cikin shirin hantsi na tashar talabijin ta Channels mai suna “Sunrise Daily”.

“Mun sake lalubo karin gawawwaki 2, abinda ya kawo adadin zuwa 5. Akwai ragowar mutane 3 da muke fatan ganowa a yau.”

A cewarsa, masu bincike na kan hanyarsu ta zuwa wurin da hatsarin ya afku, inda yace za’a dauki kwanaki kafin a iya gano tarkacen jirgin.

An tabbatar da mutuwar mutane 3 sakamakon hatsarin da ya afku a jiya Alhamis.