A wani rahoto da aka fitar ranar Litinin, wanda ke nuna wasu sakonnin email da aka kwarmata, kungiyar sa ido ta Global Witness ta ce hukumomin kamfanin Mai na Shell na sane da cewar kudaden da aka ware na yarjejeniyar sayan rijiyar Man mai lamba OPL 245, zasu fada hannun wasu manyan jami’an gwamnati ne domin amfanin kansu.
Jami’an gwamnatin dai sun hada da tsohon Ministan Man Fetur Dan Etete da kuma shugaban kasar na wancan lokacin Goodluck Jonathan.
Rijiyar Man ta OPL 245 dai anyi imanin itace rijiyar Man da tafi kowacce girma a nahiyar Afirka. An dai yi amfani da wani kamfani mai suna Malabu, wajen karkatar da kudin da aka sayi rijiyar Man dake gabar ruwan Niger-Delta.
Hukumar dake yaki da cin hanci da rashawa a Najeriya, EFCC, ta shigar da kara inda ta ke zargin kamfanin Mai na Shell da wasu kamfanoni da aikata laifin cin hanci da rashawa, sai dai ana sa ran ranar 13 a wannan wata ne kotu zata saurari karar.
A wata hira da Muryar Amurka ta yi da mataimakiyar shugaban kungiyar Global Witness shiyyar Amurka, Stefanie Ostfeld, ta ce kungiyar ta nemi ma’aikatar Shari’ar Amurka ta binciki ko kamfanin Shell ya saba dokar Amurka ta cin hanci da rashawa a duniya.