Rahotanni sun ce gwanayen ninkaya ne suka gano baraguzan jirgin a lokacin da hukumar ta NSIB take jagorantar ayyukan ceto.
Washington D.C. —
Hukumar Bincike da kiyaye hadurra ta Najeriya (NSIB) ta ce an gano baraguzan jirgin sama mai saukar ungulua da ya fadi a teku a Fatakwal da ke jihar Rivers.
A ranar 24 ga watan Oktoba, jirgin dauke da mutum takwas – fasjinja shida da matuka biyu ya fadi a yankin ruwan Bonny Finima.
Tuni dai an gano gawarwakin mutum biyar da aka tsamo daga ruwa. Kamfanin man fetur na NNPCL a Najeriya ya ce shi ne ya dauki shatar jirgin.
Cikin wata sanarwa da ta fitar, Darektar yada labarai da tallafawa iyali a hukumar ta NSIB Mrs. Bimbo Oladeji ta ce an gano jirgin ne a zurfin ruwan da ya kai mita 42 a cewar jaridun Najeriya
Rahotanni sun ce gwanayen ninkaya ne suka gano baraguzan jirgin.