Hukumomin Amurka da Holland suna binciken yadda aka yi allurai suka shiga burodi da aka hada da naman tololo, domin abinci da ake rabawa fasinjoji jiragen sama. Wan nan al’amari ya auku ne cikin jiragen sama hudu daga Amsterdam zuwa Amurka.
Ranar lahadi fasinjoji dake cikin jiragen kamfanin Delta daga Amsterdam zuwa biranen Minneapolis, Atlanta da Seattle anan Amurka suka fuskanci wan nan lamari . Mutum daya ya ji rauni, amma yaki zuwa asibiti.
Hukumar binciken manyan laifuffuka (FBI), ta Amurka tareda rundunar ‘Yansanda a Holland, talata suka ce sun fara bincike. An shirya abincin ne a wani kantin hada abincin jiragen sama dake Amsterdam mai suna Gate Gourmet a turance.
Daya daga cikin fasinjojin da ya sami allura cikin abincin sa James Tonga, ya gayawa tashar talabijin ta ABC dake nan Amurka cewa ya ji tsinin allurar cikin bakinsa.
Da aka gano alluran, nan da nan aka sakewa fasinjojin wani abinci.
Kamfanin jiragen fasinjan Delta yace yana da daukan wan nan batu da matukar muhaimmanci. Shi ma kamfanin da ya hada abincin ya kira lamarin da cewa abin “yayi matukar bakanta masa rai”.