An Gano Silar Wata Cutar Da Ta Kashe Mutane Dayawa A Afrika Ta Kudu

Wata jami'ar asibiti ta na binciken cuta

Cutar tayi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 900 tun daga watan Janairu na shekarar 2017 zuwa bana.

Jami’an kiwon lafiya a Afrika ta kudu sun gano silar barkewar cutar da ake kira Listeria, wadda ke janyo masassarar amai da gudawa, da ta yi sanadiyar mutuwar mutane 180.

Ministan lafiyar Afrika ta kudu Aaron Motsoaledi ya fadawa manema labarai shekaranjiya Lahadi cewa an gano inda cutar ta samo asali a wata masana’antar abinci dake Polokwane, a arewa maso gabashin Pretoria babban birnin kasar. Motsoaledi ya yi kira ga jama’a akan su guji cin duk wani nama da aka sarrafa don amfanin nan take, ya kuma bada umurni a dakatar da sayar da daskararren nama saboda barkewar cutar, ciki harda Polony, wani nama da ake sarrafawa a kasar.

Mozambique da Namibia sun riga sun sanar da dakatar da shigo da wadannan kayayyakin kasashen su ba tare da bata lokaci ba, yayinda Botswana da Zambia suka sanar da matakin hana sayen kayayyakin.

Shugaban kamfanin Tiger Brands, daya daga cikin manyan kamfanonin abincin Afrika ta kudu wanda kuma shi ke da masana’antar da aka ce an gano cutar, ya ce babu wata alaka tsakanin kayan abincin kamfaninsa da mace-macen da aka yi.