Kwamitoci biyu da gwamnatin jahar Zamfafa ta arewacin Najeriya mai matukar fama da matsalar ta’addanci ta kafa, sun mika rahotanninsu ga gwamnatin jahar game binciken da su ka yi kan zarge zargen da ake ma wasu manyan sarakuna biyu na hada kai da ‘yan ta’adda, da taka rawa a kashe kashen al’umma.
Sarakunan da ake zargin su ne na Zurmi da Dansadau duk a jahar ta Zamfara. Akwai kuma wani mai sarauta a yankin Birnin Magaji cikin wadanda aka bincika.
Kwamishinan Tsaro na Jahar, DIG Mamman Tsafe (murabus), shi ne ya mika wadannan rahotannin ga Mataimakin Gwamnan Jahar, Sanata Hassan Muhammad Nasiha a fadar gwamnati. DIG Tsafe y ace da shi da tsohon gwamnan jahar Zamfara, Mallam Ibrahim Wakala ne aka aza wa nauyin jagorantar gudanar da binciken. Ya ce duka kwamitocin biyu sun bi ka’idojin da aka gindaya wajen binciken. Y ace sun tattara bayanai da shaidu daga bangarorin da ke zargin sarakunan da kuma bangarorin da ke wanke su.
DIG Tsafe y ace an auna dukkan hujjojin bangaren da ke zargi da kuma bangaren da ke karewa kafin aka yanke shawara kan abin da ya fi zama daidai.
Yayin karbar rahotannin, Mataimakin Gwamnan ya ce an bayar da lokaci mai tsawo ne saboda a yi bincike mai inganci a kuma yi adalci.
Kamar yadda ba a rasa sani ba, tuni aka dakatar da wadannan Sarakunan har sai an gama bincike, lokacin da za a san makomarsu.
Saurari cikakken rahoton Sani Malumfashi:
Your browser doesn’t support HTML5