An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Sultan Muhammad Sa'ad Abubakar III

Majalisar ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter a daren ranar Litinin - agogon Najeriya.

Majalisar Kolin malaman addinin Islama a Najeriya, NSCIA, wacce ke karkashin jagorancin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Sultan Sa'ad Abubakar ta bayyana cewa an ga watan Ramadana a wasu sassan kasar.

Majalisar ta wallafa hakan ne a shafinta na Twitter a daren ranar Litinin - agogon Najeriya.

“An ga watan Ramadana a wasu yankunan Najeriya,” Shafin Twitter majalisar ya ce.

Karin bayani akan: Sarkin Musulmi a Najeriya, Muhammad Sa'ad Abubakar, Ramadana, COVID-19, Nigeria, da Najeriya.

Da ma a ranar Lahadi, majalisar ta fita da sanarwar a fara neman jaririn watan da yammacin ranar Litinin, inda ta ce idan ba a ga watan ba, sai ranar Laraba kenan za a fara azumin.

Yanzu ya zama Talata 13 ga watan Afrilu ita ce ranar azumi ta farko bisa sanarwar da ta gabata.

A baya Sarkin Musulmin ya kuma yi kira ga al’umarsa, da su kiyaye ka’idojin da aka saka na kare yaduwar cutar COVID-19 a lokacin da suke duban jinjirin watan, sannan su kuma dakata da shiga I’tikafi da tsawaita taruka saboda annobar.

Wannan shekara, ita ce ta biyu da za a yi azumin Ramadana yayin da duniya ke yaki da annobar korona wacce ta faro daga karshen shekarar 2019.

Kalli Mai Alfarma Sarkin Musulmi yana sanarwar ganin watan Ramadan:

Your browser doesn’t support HTML5

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan