An Farmaki Shelkwatar 'Yan Sanda Ta Binciken Laifuffuka Da Ke Mogadishu

Wani Sojan Somalia Bayan Tarwatsewar Bam Din Kunar Bakin Wake a Mogadishu

Wasu 'yan kunar bakin wake sun kaiwa shelkwatar binciken 'yan sanda ta manyan laifuffuka hari a Mogadishu.

Akalla mutane 13 ne suka mutu wadanda suka hada da fararen hula 5, soja 1 da kuma mahara 7 a wani harin ta’addanci da aka kai a wata harabar ‘yan sanda a Mogadishu babban birnin Somalia a yau lahadi.

Ministan cikin gidan Somalia Abdirizak Omar Mohamed ya fadawa Muryar Amurka cewa, wannan harin an auna shi ne akan shelkwatar ofishin ‘yan sanda na binciken manyan laifuffuka.

Omar yace, ‘yan kunar bakin wake ne guda biyu suka dirar wa wajen a guje da abin hawa suka rafki babbar kofar shiga ofishin CIDn, inda bam daya ya tarwatse a kofar, dayan kuma ya tarwatse a tsakiyar titi.

Daga baya kuma wasu mahara 5 da manyan bindigogi suka farwa kutsawa cikin shelkwatar, nan take aka bindige 3 a waje kan su shiga, aka kuma hallaka ragowar biyun a daidai lokacin da suka shiga harabar caji ofis din na bincike.