Kasar Jamhuriyar Benin ta soma zaman makoki na mako daya don juyayin rasuwar tsoho shugaban kasar Mathew Kerekou da ya rasu jiya Laraba.
WASHINGTON,DC —
Ba’a dai bada wani cikakken bayanin abinda ya janyo ajalin nashi ba, amma tarihinsa ya nuna cewa ya samu horaswar aikin soja ne a birnin Paris na Faransa wanda bayansa ne ya koma kasar tasu wacce a wancan lokacin ake kiranta da suna “Dahomey.”
A cikin shekarar 1972 ne Kerekou ya kwace ragamar mulkin kasar ta hanyar juyin mulki inda ya aiwatarda ita a matsayin kasar dake bin akidar Kwaminisanci, sannan ya chanja mata suna zuwa “Benin.”
Bayanda akidar kwaminisancin taki ci ne, Kerekou yayi watsi da ita, kuma ya maida kasar a bisa akidar demokradiya inda Benin ta zama daya daga cikin kasashen Afrika na farko da suka gudanarda zaben shugaban kasa na siyasa tsagaronta.
An kada shi a zaben da aka yi na 1991 amma ya sake samun nasara a 1996 inda kuma yaci gaba da zama kan karagar mulki har lokacinda sauye-sauyen da aka yi wa kundin tsarin mulkin kasar ya tilasta mishi sauka daga mulki a shekarar 2006.