Yanzu haka dai an fara zaman doya da manja tsakanin likitoci a kasar Ghana da gwamnati kuma Bello Habeeb Galadanchi ya tattauna da wakilin sashen Hausa Baba Yakubu Makeri akan wannan batun.
Bellon kuma ya fara tambayar sa ne abin da ke faruwa tsakanin likitocin da gwamnati.
Alhaji Bello wato abubuwa dake faruwa a Ghana wato ko muce babban labarin da ya dauke hankalin al’ummar Ghana shine zancen nan wanda yake ainihin Ghana suke cikin zaman zullumi domin ganinabinda zai fito akan wani taron gaggawa da shugabannin kungiyar likitoci na kasar Ghana suka yi.
Taron menene.?
Sun zauna zasu yanke shawara abinda suke niyyar yi wato zasu yi murabus baki dayan likitocin kasar Ghana dangane da cewa gwamnati ta gaza biya musu bukatun su.
Me yasa sai wannan lokaci?
Shekaru da dama Kenan su wadannan likitocin suke neman ta yadda za a yi wato a duba ainihin tsarin wato aikin su ga baki daya sun nuna cewa su aikin a matsayin na likitoci wanda yake kwararru ne ko kuma masana a fannin kiwon lafiya amma ga baki daya rayuwar su ya sabawa da irin abinda suka yi ko kuma suke yin a aikin likita wanda yake a fadin duniya ana samun likita yana daukar albashi mai tsoka sailin nan kuma da wasu alawus-alawus da suka shafi aiki dashi.
Wannan shine dalilin da yasa ainihin wato bayan kashedi da kuma irin barazana da su likitocin suka yi tun cikin shekarar bara Kenan gwamnati bata iya ta biya musu bukatu ba har ya kai wannan har ya kai wannan shekarar kuma suka yi alkawarin cewa karshen wannan wata na Yuni zasu ajiye kayan aikin su Kenan su fara wannan ba yajin aiki bane.
Ba yajin aiki bane?
Wannan murabus ne ga gabaki daya su ainihin likitocin zasu yi resingning daga wannan aikin da suke yi.
Bello Habeeb ne yayi wannan hirar.
Your browser doesn’t support HTML5