An Fara Yiwa Dalibai Gwajin Cutar SIDA a Damagaram

Hukumar yaki da cutar SIDA tare da gidauniyar uwar gidan shugaban kasar Niger Hajiya Aissata Isufu da ake kira Guri Vie Meilleur ko Kyakkyawar Rayuwa, sun kaddamar da gwajin cutar sida da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima’i, akan daliban makarantar sakandare.

A harabar makarantar share fagen Shiga jami'a wato Lyce Amadu Kuran Daga ne hukumar yaki da SIDA a karkashin jagorancin gidauniyar nan mai sunan Guri Vie Meilleur, ta uwar gidan shugaban kasar Niger Hajiya Aissata Isufu, suka kaddamar da gwajin cutar Sida da cututtukan da ake kamuwa da su ta hanyar jima'i ga dalibai.

Anyi bikin kaddamarwar a karkashin jagorancin gwamnan jihar Damagaram, da wakilan matar shugaban kasa, da hukumomin kiwon lafiya, da hukumomin gargajiya da dai sauran su, inda Gwamnan jihar bayan yayi jawabi kan muhimmanci wannan gwajin, ya kaddamar da fara aikin.

Tawagar ta garzaya makarantar Bashar Buzu inda likitoci suka fara gwajin akan dalibai maza da mata, wanda suka ce sun yi matukar farin ciki game da duba lafiyar su da hukumomi suka kudirta, yawancin su cikin doki ba tare da wani fargaba ba suka tsaya gaban likitoci don a dauki jinin su.

A nasa bangaren, daraktan hukumar kiwon lafiya na jihar Damagaram, Abu Yahya ya ce a baya an watsar da matasa a wannan fanni, an zabi makarantu ne don samun saukin isa ga matasan ganin cewa nan ne matattararsu, kuma burin gwamnati shi ne kowanne matashi ya san matsayin shi a fannin kiwon lafiya musamman SIDA da sauran cututtuka, ta la'akari da su ne manyan gobe.

Shi ma dai Tagji Musa na hukumar ilimin secondary na jihar Damagaram, ya gamsu da wannan shiri, musamman yadda yaran suka fito da bada goyon baya. Ya fadi cewa da ma a darussan da ake koya musu akwai bangaren dake koya irin wadannan abubuwan, haka ma masu wayar da kai da ake ce ma Paires Educateurs sun bi makarantu suna yiwa daliban bayani game da cutar SIDA da sauran cututtuka. Za a yi aikin gwajin har zuwa biyar ga watan Fabarairu.

Ga labari cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Yiwa Dalibai Gwajin Cutar SIDA a Damagaram - 2'58"