An Fara Tuhumar Tsohon Shugaban Sudan Da Laifukan Rashawa

A hukumance wani alkali a Sudan ya fara tuhumar tsohon shugaban Sudan Omar al-Bashir da laifukan rashawa da kuma mallakar kudaden kasashen waje ba bisa ka’ida ba.

A yau Asabar, a wata kotu dake birnin Khartoum, Bashir ya fadi cewa ya karbi kudi dala miliyan 25 daga yariman masarautar Saudiyya mai jiran gado, wato Mohammed bin Salman, amma bai yi amfani da kudin don hidimominsa ba, a cewar kamfanin dillancin labaran Reuters.

Nan take dai babu cikakken bayani akan yadda Bashir ya kashe kudaden.

Kotun manyan laifuka ta duniya da ake kira ICC a takaice na tuhumar tsohon shugaban dan shekaru 75 da haihuwa da laifuffukan yaki, da na keta hakkokin bil’adama da kuma kisan kare dangi saboda matakan da ya dauka a lokaci yakin yankin Darfur dake Sudan wanda aka dade ana yi.

Haka kuma a watan Mayun da ya gabata aka fara tuhumar Bashir da laifin zuga, da kuma taka rawa a kisan wasu masu zanga-zanga da suka caccaki gwamnatinsa.