A jiya Talata aka fara taron majalisar manoma ta Najeriya karo na 43 a Umuahiya hedikwatar jihar Abia da ke kudu maso yammacin Najeriya, don inganta noma da kuma bunkasa tattalin arzikin kasa.
Da yake jawabinsa a gurin taron, Dakta Aminu Babandi, wanda ya wakilci Dakta Mohammed Bello Umar, babban Sakataran Ma’aikatar Noma na Tarayya ya ce, dole ne a bunkasa noma tare da tabbatar da cewa mun kirkiro shirye-shiryen da za su samu goyon baya a matakan jihohi da kuma tarayya.
Babandi ya kuma kara da cewa suna duba gurare guda uku inda za su fi mayar da hankali.
Shima Kwamishinan Noma na jihar Abia, Barista Chinedum Elemchi, ya bayyana farin cikinsa lokacin da yake jawabin bude taron, inda ya ce gwamnati tasha kaddamar da shirye-shirye a kokarinta na inganta harkar noma a duk fadin kasar.
Sannan ya kuma ce ya kamata a tattaro sakamakon wadannan shirye-shiryen don dubasu da kyau domin bunkasa tattalin arziki da kuma samar da aikin yi.
Haka kuma taron ya samu halartar mutane daga fannoni daban daban na rayuwa a kokarin da ake na tsara dabarun inganta noma don bunkasa tattalin arzikin kasar.
Saurari cikakken rahoton Alphonsus Okoroigwe:
Your browser doesn’t support HTML5