An fara taron kolin kungiyar hada kan kasashen Afirka tareda kira ga wakilan kungiyar su dauki mataki na tunkarar fitinu da suke kunno kai a sassan nahiyar.
Shugaban kungiyar Jean Ping yayi kira ga shugabanin kasashe dake nahiyar su dauki matakai na warware matsalolinsu da kansu.
Taron kolin zai maida hankali ne kan tsaro d a kuma cinikayya.
Tarayyar Afirka tace sai tayu ta tura sojoji domin yaki d a ‘yan tawaye da Jamhuriyar demokuradiyyar kwango. Haka kuma tana goyon bayan shirion kungiyar ECOWAS na tura dakaru domin zuwa Mali domin su yaki mayakan sakai a arewacin Mali masu da’awar Islama.
Haka taron kolin zai yi kokarin warware rikicin shugaban kungiyar.
Ping yana fuskantar kalubale daga minister harkokin cikin gida ta Afirka ta kudu Nkosazana Dlamini-Zuma. A karawar su ta farko a watan janairun bana babu daya cikin ‘yan takarar biyu da ya sami rinjaye na kshi 2/3 na kuri’u domin zama shugaba.