Batun kare giwaye da karkanda sune muhimman batu a babban taro na kungiyoyi da suke rajin kare yarjejeniyar kare dabbobin da za'a fara Asabar a Afirka ta kudu.
A dai dai lokacinda ake fara wannan taro a birnin Johannesberg, kan fataucin gabban dabbobi da suka kusan bacewa, daruruwan masu zanga zanga ne suka hallara a birnin na Johannesberg domin nuna adawa da kudirin da Zimbabwe da Namibia suke goyon baya, na neman amincewa a yi cinikin hauren giwaye bisa hanyoyin da aka amince da su.
'Yar karamar kasar Swaziland, ita ma ta gabatar da kuduri na kyalewa a yi cinikin kahon karkanda.
Mai masaukin baki Afirka ta kudu tana goyon bayan duka kudurorin biyu, tana mai cewa cinikin wadannan gabba ko wasu bangoagorin dabbobin, zai taimakawa shirin kare dabbobin, kuma ya taimkawa tattalin arzikin kasashen.
Amma suna fuskantar matukar adawa daga galibin wakilan kungiyoyi ko kasashe 183 da suka amince da yarjejeniyar.