Wani mai tsokaci kan al’amuran yau da kullum da ke garin Kaduna mai suna Mallam Isyaku Alhassan Kauran Mata ya ce tsarin diflomasiyya na bukatar Shugabannin kasashe su rinka tafiye-tafiye da ziyarce-ziyarcen juna. Ya ce to amma Shugaban Najeriya Muhammadu Bahuri ya cika tafiye-tafiye. Ya ce tafiye-tafiye na da kayu to amma idan ya yi yawa bai da amfani. Ya ce Buhari ya shiga sahun Shugabannin Afrika da ke ganin dole sai sun samu yaddar wasu kasashen Yammacin duniya kafin su iya cimma abin da su ke son cimmawa.
Alhaji Kauran Mata ya ce ya kamata ace Shugaba Buhari na tura wasu daga cikin mukarrabansa su wakilce shi a wasu daga cikin irin wadannan tafiye-tafiyen, amma ba wai shi da kansa ya rika tafiya ba.
Da ya juya kan wasu nasarorin da aka samu a farkon kafuwar wannan gwamnatin, Kauran Mata ya ce ko su ma sun a da nasaba da dan zaman da Buhari ya yi a gida. Y ace Buhari na fara tafiye-tafiye sai abubuwa su ka fara sukurkucewa., sun a komawa kamar yadda su kea da.
Ga cikakkiyar tattaunawar:
Your browser doesn’t support HTML5