ZABEN2015: An Fara Siyar da Katin Zabe a Najeriya

An kama wani mutun mai siyar da katin zabe a jihar Bauchi, a dai-dai wannan lokaci da aka tunkari babban zabe na shekarar 2015 a Najeriya.

Yanzu haka dai ana cigaba da raba katin zabe na din-din-din a jihohin Najeriya, kuma hukumomi na iya bakin kokarin su don gani an ilimantar da jama’a dangane da mahimancin karbar wannan kati da kuma yin amfani dashi yadda ya kamata.

Wani labari da muka samu na cewa wasu mutane suna karbar katunan ‘yan’uwansu wadanda basu kusa balle su karba, a sanadiyyar haka yasa wasu suna amfani da wannan dama don sayar da wannan kati ga masu bukata.

Yanzu haka dai an kama wani mutum a Jihar Bauchi yana siyar da katin zabe na din-din-din ga wasu mazauna yankin nasu. Kuma yanzu haka dai yana fuskantar tuhuma a hannun ‘yansanda.

Your browser doesn’t support HTML5

Katin zabe a Najeriya - 1.19"