An Fara Shirin Samar Da Zaman Lafiya a Yankin Zuru

Sufeto Janar Mohammed Adamu

Yawaitar kisan gilla tsakanin bangarorin dake gaba da juna a yankin Zuru na jihar Kebbi na ci gaba da haifar da zaman zullumi ga ilahirin al’ummar da ke masarautar Zuru.

A kokarin samo bakin zaren warware wannan rikici babban sufeton ‘Yan Sandan Najeriya, Muhammad Abubakar Adamu, ya jagoranci zaman tattanawa tsakanim bangarorin biyu.

Bangarorin dake gaba da juna a yankin Zuru sun hada da Fulani da Dakarkari, inda kowanne bangare ke zargin daya bangaren da yin kisan gilla ga mutanensa, ba tare da an hukunta mai laifi ba.

Zaman da babban Sufeton ‘Yan Sandan Najeriya ya jagoranta, ya samar da dama ga kowanne bangare ya fadi korafe-korafensa da manufar hanyar da za a samar da zaman lafiya.

Da yake bayyana dalilin kiran wannan taro, shugaban ‘Yan Sandan ya ce, shugaban kasa Muhammadu Buhari ya damu da halin da yankin Zuru yake ciki, shiya sa ya aika shi domin zama da dukkan bangarorin domin nemo hanyar gyara.

Wasu mazauna yankin daga bangarorin biyu sun bayyanawa sashen Hausa na Muryar Amurka halin da wannan yanki ke ciki, inda kowanne bangare ke daura laifi akan daya bangaren.

Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Muhammad Nasir.

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Shirin Samar Da Zaman Lafiya a Yankin Zuru - 3'01"