Baya ga haramta ziyara ga daurarru, hukumomin kula da gidajen yari da kuma gyaran hali na Najeriya sun ce suna daukar matakan da suka kamata, musamman batun nan na samar da tazara a tsakanin al’umma da kuma gindaya sharudda ga lauyoyin da ke muradun ganawa da wadanda ake tuhuma.
Malam Misbahu Lawan Kofar Nasarawa, wanda shi ne kakakin hukumar a Kano, yayi wa Muryar Amurka karin haske game da matakan zamantakewa tsakanin daurarru.
"Idan za su yi alwala sai sun sa sinadarin kashe cuta a hannu wato hand sanitizer, idan za su shiga daki ma sai sun sa, kuma idan aka kawo sabbin mutane sai an tsaftace su sa'annan kuma a sake ware su na tsawon kwana 7, domin a tabbatar ba su da komai," a cewar kakakin.
Ita-ma hukumar ‘yan sanda ta Najeriya ta ce tana daukar nata matakan domin kare wadanda ake tsare dasu a ofisoshin ‘yan sanda daga wannan cuta ta Coronavirus.
Kakakin rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya ce "wadanda suka aikata kananan laifuka duk an bada belinsu saboda a rage cunkoso."
Hakan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da Majalisar Malamai ta jihar Kano ke kira ga hukumomi su kara kaimi wajen kare al’umma daga wannan annoba ta Corona.
Saurari cikakken rahoton a sauti.
Your browser doesn’t support HTML5