An Fara Sa Ido Kan 'Yan Wasa, Gabanin Budewar Kasuwar 'Yan Wasan

Tsoho kocin kungiyar kwallon kafa ta Arsenal dan kasar Faransa Arsene Wenger, na bukatar dawowa cikin masu horas da 'yan wasa. Ita kuwa kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich, tana la'akari da ganin shi a matsayin wanda zai maye gurbin Niko Kovac.

AC Milan ta janye damarta kan sayen dan wasan baya na kungiyar kwallon kafa ta Chelsea Gary Cahill, mai shekaru 32 da haihuwa.

Har ila yau manajan kungiyar ta AC Milan Gennaro Gattuso, yace har yanzu bai cire rai na dauko dan wasan gaba na LA Galaxy ba mai suna Zlatan Ibrahimovic, dan kasar Sweden, mai sherkaru 37 da haihuwa.

Ku Duba Wannan Ma Manyan Kungiyoyin Kwallon Kafa Na Duniya Sun Shiga Riga Daya

Manchester United da Tottenham suna bibiyan dan wasan baya na Sampdoria, mai suna Joachim Andersen, dan shekaru 22 a duniya.

Kungiyar Chelsea ta tura tawagarta don sanya ido kan matashin dan wasan tsakiya me fafatawa a kulob din Brescia, mai buga Seria B mai suna Sandro Tonali. Inter Milan itama tana sha'awar sayen matashin dan wasan dan shekaru 18 a duniya.

Borussia Dortmund tace zata sayar da dan wasan gefenta, dan kasar Ingila Christian Pulisic, wa kungiyar Chelsea ko Liverpool, amman sai dan wasan ya amince da zama a kungiyar zuwa karshen kakan wasa na bana.