An Fara Kokowar Gargajiya A Kasar Nijar

Kokowa a Jamhuriyar Nijar

Ministan matasa, wasannin motsa jikin da al'adu na kasar Nijar, Malam Kasim Mukhtar, ya kaddamar da buda shagulgulan kokowar gargajiya karo na talatin da tara, (39) a Damagaram, inda ‘yan kokowa na jihojin jamhuriyar Nijar, za su kara har tsawon kwanaki goma don samun zakaran da zai dauko takobi.

Mauduin da aka dauka a bana shine gudurmawar matasa a tsarin farfado da kasar Nijar, wanda al’adu na taka mahimmin rawa a cikinsa.

Yahaya Muhammad shugaban kwamitin tsara kokowar ya ce a bana jama’a zasu ga kokowa mai ban sha’awa kuma cikin kyakkyawan tsaro da kuma wani sabon tsari na saka kokowar nakasassu a ciki a bana domin suma a dama dasu.

Ya kara da cewa za a tabbatar da ganin cewa an magance kura kuran da suka faru a baya domin cigaban kokowa a kasar Nijar.

A kokowar ta yau Dosso ta kara da Diffa Maradi da Tillaberi, Dosso ta tashi da kaye shida Diffa kaye uku mutuwar kasko daya.

Your browser doesn’t support HTML5

An Fara Kokowar Gargajiya A Kasar Nijar - 3'55"