An Fara Karantar da Yara 'yan Gudun Hijira a Sansanoninsu

Hukumar bada agaji da gwamnatin tarayya sun fito da wani shiri na bude makarantu a sansanonin 'yan gudun hijira, don kada a bar yaran da rikicin 'yan boko haram ya shafa a baya.

Alkaluman hukumomin bada agaji sun nuna cewa yanzu haka dai akwai yara fiye da dubu goma da hare-haren ‘yan boko haram ya raba da makarantunsu, abinda ke zama babban barazana ga cigaban ililin Najeriya.

Sai dai kuma wani sabon yinkuri na ganin cewa ba a bar yara ‘yan gudun hijira ba karatu ba, ya sa hukumomin bada agajin gaggawa bude azuzuwan karantar da yaran a sansanonin ‘yan gudun hijira.

Alhaji Sa’adu Bello mai kula da sansanonin ‘yan gudun hijiran birnin Yola a jihar Adamawa, ya fadi cewa an bude makarantun ne don taimaka ma yaran da rikicni ya shafa don kada a bar su a baya. Ya kuma ce gwamnatin tarayya ta yi wani shiri na taimaka ma yaran, kuma shirin ya kunshi tanade-tanaden da za a iya canza ma yaran wuraren da suka fi dacewa don samun yin karatu.

Samun dorewar wannan shirin yasa yanzu haka aka tanadi malamai da ‘yan sa-kai bayan hadin guywar da ake yi da wasu hukumomi don tabbatar da cigaban shirin.

Your browser doesn’t support HTML5

'yan gudun hijira - 3'02"