An fara Gutsiri Tsoma akan Wasu Kudi da Tsohon Prime Ministan Nijar Shehu Amadu Ya karbo.

  • Ladan Ayawa
Niger taci bashi lokacin rikon kwarya na Shehu Amadu

Sakamakon wasu kudade da gwamnatin Shehu Amadu ta karbo aro a shekarar 1990 ya fara kawo tada jijiyan wuya.

Ga dai bayanin da shugaban gidan rediyon Niyya a birnin kwanni Haruna Mammam Bako yayi wa sashen Hausa.

Bello kuma ya tambaye shi ne yadda batun yake?

Niger taci bashin ne lokacin rikon kwarya na Shehu Amadu ne da kuma lokacin mulkin muhammam Usman to rikici ya tashi yanzu maganar ta taso su a mataki na kasa yan adawan suna gani suna ma Usman din ne ake son a shafa masa kashin kaji domin a hana shi tsayawa takarar zabe a cikin Niger din a labaran dake bazuwa ta riga ta zuba kusan miliyan 5 na bola a cikin miliyan 20 da zata zuba mata wanda dai wannan maganar ya kai karshe.

Shi Shehu Amadun wanene shi?

Yanzu shine mai sasantawa na kasa can da shi yayi Prime Minister rikon kwarya lokacinda Niger ta fito daga taro na kasa wanda ake cewa Comfere Nationala shekarar 1991.

Kuma shine ya shirya zabubbuka na farko wanda shi Muhammadu Usman ya zamo shugaban kasa a lokacin.

Your browser doesn’t support HTML5

Jamhuriyar Nejar - 1'55"